Our Programs

Explore a variety of shows that celebrate culture, education, and wholesome entertainment for the family.

INGANTA TILAWA

"Inganta Tilawa" Captivates a 50-minute interactive program that delves into the timeless art of Qur'anic recitation. This educational and inspirational show offer viewers a unique opportunity to explore the beauty and significance of reciting the Qur'an. With a blend of expert guidance, live demonstrations, and audience participation.

Inganta Tilawa shirine na minti 50 dake zuwa duk sati don koyar da ingantanciyar tilawar alkurani daga kwararrun malamai. Wannan shiri na mussamman babbar damace ga masu shaawar koyan karatun alkurani ta inda zasu hadu kwarrarun malamai masana alkurani kai tsaye.

TSANGAYAR TAFSIRAI

"Tsangayar Tafsirai" is a captivating 50-minute daily Tafsir lesson program that provides viewers with a unique opportunity to immerse themselves in the profound world of Quranic interpretation. Set in different mosques across Nigeria, this enlightening show features prominent Islamic scholars who deliver live Tafsir lessons.

Tsangayar Tafsirai Shirine na minti 50 dake zuwa kowacce rana in da zakulo fitattun majilisan tafsirin alkurani mai girma daga manyan masallatai daban daban dake fadin Nigeria. Wannan shiri zai baiwa masu kallo damar zai amfana da sanin maanonin ayoyin alkurani daga bakin kwararrun malaman kasar Hausa.

ILMI DAGA TUSHE

"Ilmi Daga Tushe" is an educational program that brings the classroom to viewers' homes four (4) times a week, with a focus on the Nigerian syllabus for basic education and Islamic Studies. This interactive show is tailored for beginners, providing demonstrated lessons in essential subjects, both within the standard educational system and Islamic studies.

Ilimi daga Tushe shiri ne na minti 30 dake zuwa sau hudu duk sati wanda ke gudana ta sigar ajin makaranta na musamman, shirin yana maida hankali wajen karantar da manhajar karatun ilimin boko da addini ta bai daya na hukumar ilimin Nigeria wato UBEC. Shirin damace ga masu son fara karatu a matakin farko su amfana da ingantaccen ilimin zamani da addinin islama dai da manhajar karatun Nigeria.

TASKAR MA'AIKI

"Taskar Ma'Aiki" is a concise 30-minute individual program that embarks on a captivating journey into the realms of Hadith science and Fiqh al-Sunnah. This enlightening show is designed to provide viewers with a deeper understanding of the traditions and teachings of the Prophet Muhammad (peace be upon him).

Taskar Maiaki shirine na minti 30 dake zuwa duk sati wanda kwararran Malamin hadisi ke gabatar da darasi mai zurfi akan Ilimin hadisi ta fannonin sa guda biyu; Fannin riwaya: Wanda ta hanyarsa ne ake sanin ingancin hadisi ko rashin ingancin sa. Fannin diraya: wato sanin Ilimi da fikihun da hadisin ya kunsa. Wannan shiri damace ta musamman ga daliban Ilimi masu tasowa da zasu sami kyakkyawar shinfida ta sanin sunnar maaiki daga bakin kwararrun malaman wannan fanni.

ZAUREN MALAMAI

"Zauren Malamai" is a daily 50-minute lesson program that invites viewers to embark on a spiritual journey within the hallowed walls of selected mosques across Nigeria. Renowned scholars deliver insightful lessons, drawing from an array of foundational Islamic books, including Fiqh, Hadith, Aqidah, and other fundamental texts delivered by our esteemed scholars, nurturing the souls and minds of our audience.

Zauren Malamai shirine na minti 50 dake zuwa akullum wan da ake dauko zababbun karatukan manyan littatafan musulunci na fannoni daban daban kamar Fiquhu, Tauhidi, Hadisi wanda shahararrun malamai ke gabatarwa a masallatansu da majilisansu na Ilimi dake fadin Nigeria da makwabtanta. Shirin na taimakawa kwarai da gaske wajen yada ilimin addini da sanin manyan litttafan musulunci a cikin al’umma.

KUNDIN TARIHI

"Kundin Tarihi" is a captivating 50-minute program that presents a rich tapestry of voice-overs and insightful interviews, dedicated to the life and legacy of Prophet Muhammad (SAW) and general Islamic history.

Kundin Tarihi shirine na minti 50 dake zuwa duk sati da ya ake bada ingantaccen tarihin musulunci tun daga rayuwar manzon SAW har izuwa faduwar daular Usmaniyya. Ana gabatar da shirin ta hanyoyi daban daban (Hira da masana tarihi, Karanta rubutaccen tarihi tare da nuna hotuna da bidyon tarihin musulunci.)

TAFARKI MADAIDAICI

"Tafarki Madaidaici" is a 50-minute discussion program that serves as a platform for engaging conversations on Islamic creed, as well as the vital topic of countering extremism. This enlightening show is dedicated to sensitizing viewers on the principles of Islamic faith, while addressing the challenges posed by deviant beliefs and false myths that can lead to extremism. Through informed discussions and expert insights,

"Tafarki Madaidaici" offers valuable guidance on promoting a balanced understanding of Islam and safeguarding against radicalization. Tafarki Madaidaici shiri ne na minti 50 da ake tattaunawa acikinsa duk sati don fito da ingantacciyar akidar musulci tare da bayanin baragurban akidun da aka cuso cikin addinin musulunci da suke haifar da rarrabuwar kai da zafin addini. Shirin na kokarin fito da kyakkyawar surar musulci ta hakika wanda ke kira ga hadin kai da kaunar juna da zaman lafiya tsakanin musulmai dama wadanda ba musulmai ba.

MAGADA ANNABAWA

"Magada Annabawa" is a 50-minute interview program that delves into the fascinating personal biographies of distinguished scholars, providing viewers with a unique insight into their remarkable journeys in da'wah, scholarly pursuits, and their impact on the nation and the wider Islamic world.

Magada Annabawa shiri ne na minti 50 da ake gabatar dashi ko wane sati inda ake gayyato shararrun malaman Nigeria a tattauna dasu kan tarihin rayuwarsu ta neman Ilimi da gwagwarmayarsu ta da’awa da kuma gudunmuwar da suke bawa alumma a fannoni daban daban na rayuwa. Shirin kai baiwa malaman dama wajen fito da ra’ayoyin su akan shugabanci, siyasa, tattalin arziki, tsaro da sauran alummuran yau da kullum a fadin duniya.

IBADA DA HUKUNCI

"Ibada da Hukunci" is a 50-minute discussion program that provides a comprehensive exploration of Islamic jurisprudence (Fiqh) and the issuance of Fatwa (religious rulings). This enlightening show delves into the intricate aspects of Islamic law and religious guidance, offering viewers a deeper understanding of how Fiqh principles are applied to real-life situations.

Ibada da Hukunci shiri ne na minti 50 dake zuwa mako mako don gabatar da muhimman darussa da bayanin hukunce hukuncen musulunci kan ibada da mua’mala. Shirin kan amsa tambayoyin masu saurare da bada fatawa daga sharararrun malaman fiqhu. Shirin zai tai makawa mai kallo wajen sanin yadda zai aiwatar da ibada a aikace.

AHLUL-BAITI DA SAHABBAI

"Ahlul-Baiti da Sahabbai" is a 50-minute discussion program that offers a deep exploration of Ahlul-Bait and Sahaba history, focusing on the genuine accounts of the Sahaba (Companions of the Prophet) while debunking false claims and narratives associated with them. This enlightening show highlights the strong and harmonious relationship between the Sahaba and Ahlul-Bait, providing a well-rounded perspective on their interactions and the significant role each played in the early Islamic community.

Ahlulbaiti Da Sahabbai shiri ne na minti 50 da ke zuwa duk sati da ake tattaunawa mai zurfi kan tarihin sahabbai da ahalulbaiti. Shirin na maida hankali kan ingantaccen tarihin Sahabbai da ahalulbaiti da fito da kyakkayawar alaka mai karfi dake tsakaninsu tare da kore tarihin karya da ake jinginawa garesu. Wannan shiri dama ce ga masu kallo don sanin gudunmawar da shahararrun sahabbai da ahlulbaiti suka baiwa duniyar musulunci.

MUSAYAR BASIRA

MUSAYAR BASIRA is a 50-minute television program that serves as an Entrepreneurship talk show and a showcase of the training, creativity, innovation, technology, and productivity within various business and industries. This engaging TV program is designed to provide viewers with valuable insights into the world of entrepreneurship and the dynamic landscape of businesses and industries.

Musayar Basira shirine na minti 50 dake zuwa duk sati don horar da matasa dabarun dogaro da kai ta hanyar koya musu sana’oin hannu, kirkire kirkire da salon kasuwanci da yadda ake kafa kananan masana’antu da gudanar da su. Wannan shiri damace ga masu kallo da zasu sami horarwa kyauta a fannoni daban daban na sana’oi da kasuwanci.

NI DA IYALINA

"Ni da Iyalina" is a dynamic 50-minute program that combines short dramas, public interviews, and studio discussions to address the vital aspects of family counseling and lifestyle. This engaging show offers viewers practical insights into enhancing family dynamics and improving their overall quality of life.

Ni da Iyalina shiri ne na minti 50 dake zuwa duk sati cikin siga daban daban kamar dan gajeren wasan kwaikwayo, Jin ra’ayin maurata a gidajen su da tattaunawa da kwararru cikin studio, shirin na maida hankalin wajen bada shawarwari da dabarun zamantakewar aure da magance matsalolinta.

TURAKAR MATA

TURAKAR MATA is a 50-minute dialogue program dedicated to addressing topical issues related to women's affairs in Northern Nigeria. This program provides a platform for open discussions, analysis, and exploration of the challenges, opportunities, and the overall status of women in the region.

Turakar mata shiri ne na minti 50 duk sati da aka kebance shi ga mata don basu damar tattaunawa kan lamuran addini da zamantakewa da suka kebanci mata a Nigeria. Hakanan shirin na kokarin tattaunawa kan manyan kalubalen da ‘yanmata ke fuskanta gabanin aure kamar rashin samun ilmi da jinkirin samun mijin aure da kuma matsalolin rayuwar aure ko ta zawarci. Hakanan shirin na nazari kan kalubalen rashin samun yanayin aiki mai kyau daya dace da mata a kasuwanni da guraran aiki.

AL’UMMA TAGARI

AL’UMMA TAGARI is a thought-provoking 50-minute dialogue program dedicated to addressing and finding solutions to pressing social problems. The program distinguishes itself by focusing on issues related to our way of life within the capacity of our society, without relying on government intervention. It offers a platform for in-depth discussions, analysis, and debate on various societal challenges and how these can be resolved at the community and individual level.

Alumma ta gari shiri ne na minti 50 da ke zuwa duk sati da yake mai da hankali wajen nazari kan matsalolin rayuwa da suka dabai baye alumma da kuma samo musu hanyoyin warware su a tsakanin alummar ba tare da an dogara da gwannati ba. Masu kallo zasu amfana da nazari mai zurfi da dabaraun warware matsaloli ta hanyar damammakin da ke kewaye dasu.